Hukumomin Saudiyya sun dau mata da yi mu su horo irin na soja don aikin gadi da taimakawa alhazai mata a masallacin Manzon Allah a Madina.
Yanzu dai zaratan jami’an su 113 a Madina inda za su rika aiki koyaushe wato dare da rana a rukunin mata 18.
Tsarinan yi shi ne don kara ba wa mata dama su nuna basirar su ga hidima ga al’umma da lamuran alhazai.
Akwai ma irin jami’an da ke aiki a Makkah inda su kan tallafawa maniyyata.
Duk da yanayin aikin tsaro su ke yi, mata na da kamala daidai gwagwado da ta bi tsarin addinin Islama a yayin gudanar da wannan aikin.
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
Thank you for every other great post. Where else may anyone
get that kind of info in such a perfect way of writing?
I’ve a presentation subsequent week, and I am on the look for such information.