• Sun. Jan 16th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

SAUDIYYA TA DAU HOTUNA FIYE DA DUBU NA HAJARUL ASWAD TA NUNAWA DUNIYA

A karo na farko Saudiyya, ta baiyana yanda dutsen nan mai daraja HAJARUL ASWAD da ke makale a jikin dakin Ka’aba ya ke ta hanyar daukar fiye da hotuna 1000 da amfani da fasahar kamara mai karfin dauka fayau “49,000 megapixel” don ganin asalin yanda dutsen ya ke.

Hakanan an dauko hoton matakin shaidar sawun Annabi Ibrahim MAKAMA IBRAHIM don nuna yanda wajen ya ke da muhimmancin sa a tarihi.

An shafe sa’a 7 a na daukar hotunan kuma zai kai tsawon sati daya a na daidaita su.

Dutsen dai da ke da kalar ja, na manne ne a kusurwar kudu maso gabashin dakin ka’aba.

A kan fara dawafi a daidai saitin dutsen na Hajarul Aswad kuma a tarihi Manzon Allah Muhammad mai tsira da aminci ya kafa dutsen a inda ya ke yanzu bayan wani aiki na gyara da a ka yi a dakin.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *