• Fri. Dec 2nd, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari...

SAUDIYYA TA CE BA TA GA WATA BA DON HAKA LITININ CE KARAMAR SALLAH

Babbar hukumar Saudiyya ta baiyana cewa ba a ga watan shawwal ba a ranar asabar a kasar don haka sai litinin din nan za a yi karamar sallah.
Sanarwa ta baiyana cewa an duba ba a ga wata ba don haka za a cika azumi kenan na hijira 1443 ya zama 30 cif.
Sarki Salman ya shigo Makkah don ganin karshen watan ramadan na bana.
Sarkin ya shigo fadar Alsafa da ke daf da haramin Makkah inda zai zauna har idin karamar sallah a nan masallacin dakin Ka’aba.
An ga Sarkin na sallah a nan babban masallacin kuma ya taho Makkah ne daga Jeddah.

KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
One thought on “SAUDIYYA TA CE BA TA GA WATA BA DON HAKA LITININ CE KARAMAR SALLAH”
  1. It is really a nice and helpful piece of info. I am happy that you just shared this helpful information with us. Please stay us informed like this. Thanks for sharing.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *