• Mon. Jan 17th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

SAUDIYYA TA BUKACI A FARA DUBA WATAN RAMADAN A LAHADIN NAN

ByNoblen

Apr 10, 2021

Saudiyya ta bukaci al’umma su fara duba watan ramadan daga ranar lahadin nan don shirin azumin ramadan na hijira 1442.

Hukumar Saudi ta ce duk wanda ya ga wata a lahadin ta ganin ido ko amfani da na’urar hangen nesa, to ya sanar da hukuma mafi kusa.

Watan hijira na kwana 29 ko 30 don haka a ke duba sabon wata idan wata ya cika kwana 29.

A Saudiyya watan sha’aban na cika kwana 29 a lahadin nan.

A na sa ran fara azumi ranar litinin ko talata.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *