• Sat. May 21st, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

SAUDIYYA NA SHIRIN SANAR DA MATSAYIN SHIRIN AIKIN HAJJIN BANA

ByNoblen

Jun 9, 2021 , ,

Hukumar Saudiyya na shirin baiyana matsaya kan shirin gudanar da aikin hajjin bana a ‘yan kwanaki.

Sanarwar za ta faiyace yiwuwar tafiya hajjin daga alhazan kasashen ketare ko kuma akasin hakan.

Mukaddashin ministan labarun Saudiyya Dr.Majid Al-Qasabi ya baiyana cewa kasar na gudun kar taron aikin hajji ya zama wajen yada cutar korona bairos ga kasar da duniyar musulmi.

Wannan bayani na fitowa ne kasa da kwana 40 gabanin tsayuwar Arfa.

Wata sanarwa daga ma’aikatar lafiya ta  Saudiyya na nuna za a ba da dama ga alhazai dubu 45 daga ketare su shiga kasar don gudanar da aikin hajji.

Jami’an hajji aun hakikance ko aikin hajjin zai yiwu, to zai kasance da ‘yan alhazai kalilan ne aiunun.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
42 thoughts on “SAUDIYYA NA SHIRIN SANAR DA MATSAYIN SHIRIN AIKIN HAJJIN BANA”

Leave a Reply

Your email address will not be published.