• Mon. Jan 17th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

SAUDIYYA NA BUKATAR TAKATSANTSAN A KASUWAR FETUR TA DUNIYA

ByNoblen

Apr 2, 2021 , , ,

Saudiyya na bukatar takatsantsan ga yawan gangar fetur da a ke hakowa a kullum a tsakanin kasashe 23 membobin kungiyar kasashe masu arzikin fetur ta duniya OPEC.

Ministan fetur na Saudiyya Yarima Abdul’aziz bin Salman ya baiyana haka gabanin gagarumin taron kungiyar.

A waran jiya OPEC ta amince da hakar kashi 113% na man fetur don sayarwa a kasuwar duniya.

Yarima bin Salman ya ce face an samu bayanai na tabbacin farfadowar lamura, to takatsantsan din shi ne mafi a’ala.

Hakanan ya ce Saudiyya na tunanin dawo da hakar ganga miliyan daya da ta rage don kashin kai a yunkurin daidaita farashin na fetur.

Tunanin dai na ‘yan OPEC shi ne yiwuwar ba da damar kara hako ganga 500,000 ga yawan adadin danyan man da a ke hakowa.

Rage yawan fetur da a ke hakowa kan ba da tashin samun darajar sayar da danyen man.

Saudiyya na kan gaba a kasashe mafiya yawan arzikin fetur a duniya.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *