• Sun. Jan 16th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

SAUDI TA MUSANTA RADERADIN BARAZANA GA LAFIYAR MAI BINCIKE KAN KISAN JAMAL KASHOGHI

Saudiyya ta musanta raderadin da ke nuna kulla cutar da mai bincike na majalisar dinkin duniya ga yanda a ka yi wa dan jaridar nan na Saudiyya Jamal Kashoggi kisan gilla a karamin ofishin jakadancin Saudiyya a Istanbul na Turkiyya.

Jagorar binciken kisan gilla ta majalisar dinkin duniya Agnes Callamard ta ce an yu ma ta barazanar kisa matukar ta zurfafa bincike kan batun kisan na Kashoggi.

A lokacin majalisar dinkin duniya ko ita kan ta Agnes ba su baiyana jami’in Saudi da a ke zargi da barazanar ba.

Yanzu dai jami’in wanda shi ne shugaban kare hakkin ‘yan adam na Saudi Awwad Alawwad ya ce shi ne mutumin da a ke magana kuma sam abun da ya fada babu nufin barazana ga rayuwar wani.

Alawwad ya ce ba zai tuna abun da ya fada da ya kawo zargin ba fiye da shekara da ta wuce, amma ba zai taba yiwuwa ya yi wa wani ko wata barazana haka ba.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *