• Sun. Nov 28th, 2021

Noblen tv

Gaskiya Jari…

SATAR MUTANE YA TA’AZZARA A KADUNA

A kusan duk mako ko ma wani lokacin duk kwana biyu sai ka ji an sace wasu matafiya ko ‘yan makaranta a yankin jihar Kaduna.

Fitar da dan sa da gwamnan Kaduna Nasiru Elrufai ya yi daga makarantar gwamnati don gudun kar a sace shi, na nuna yanda lamarin ya ke neman gagarar magancewa.

Matukar dai mutum ya bi hanyar mota daga Abuja zuwa Kaduna har ma Zaria, sai dai ya lizimci addu’a don gudun fadawa tarkon barayin marar sa imani.

Zuwa yanzu hatta yunkurin sulhu ko tuntubar barayin bai samu gagarumar nasara ba, don tamkar kara bullo da dabarun satar mutanen a ke yi.

Hanya mafi natsuwa ita ce ta jirgin kasa tsakanin Abuja da Kaduna don jami’an tsaro kan raka fasinjoji.

Akwai kuma masu sharhi da ke nuna yiwuwar hadin baki da wasu a cikin gari da kan sanya annobar satar kasa karewa.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *