• Mon. Jan 17th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

SATAR MUTANE KAN HANYAR ABUJA ZUWA KADUNA NA NEMAN KARYA TATTALIN ARZIKIN GARIN MU-SALANKEN JERE

ByNoblen

Dec 25, 2021 , ,

Masarautar Jere a karamar hukumar Kagarko a jihar Kaduna ta ce satar mutane kan hanyar Abuja zuwa Kaduna na neman kawo zagon kasa kan tattalin arzikin al’ummar yankin.
Garin jere dai wanda ke rabin tafiya tsakanin Abuja da Kaduna na da yawan jama’a da ma kasuwa.
Da ya ke magana a madadin masarautar a ziyarar da ya kawo ofishin Muryar Amurka da tawagar sa, Salanken Jere Alhaji Hamza Yakubu ya ce ma su jin labarin garin daga nesa kan yi dari-dari don zullumin barayin mutane alhali ba maboyar su a garin da kewaye.
Salanken ya ke har wasu na ba da shawarar a kawar da garin ya koma barikin soja matukar za a samu tsaro.
Shugaban kwamitin tsaro na sirri na majalisar wakilai Sha’aban Ibrahim Sharada, ya ce shugaba Buhari na iya bakin kokarin sa don aminta dukkan yankin arewa maso yamma amma sai mutane sun ba da goyon baya matukar a na son samun gagarumar nasarar magance miyagun irin.
A nan Salanken Jere ya ce labaru marar sa sahihanci kan garin na su sun sa firgita masu zuba hannun jari.
Duk da mutane kan yi amfani da jirgin kasa don samun tsaron sufuri tsakanin Abuja da Kaduna, amma har yanzu masu tafiya a mota su ne mafiya yawa kuma su kan wuce ne cikin dar-dar da hakan kan sa da zarar wata mota ta rage gudu sai na baya su nemi jan birki don rashin sanin tabbas.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
8 thoughts on “SATAR MUTANE KAN HANYAR ABUJA ZUWA KADUNA NA NEMAN KARYA TATTALIN ARZIKIN GARIN MU-SALANKEN JERE”
 1. Hello my family member! I wish to say that this
  post is amazing, great written and include approximately
  all important infos. I would like to see more posts like this .

 2. I do consider all of the ideas you have presented for your post.
  They’re really convincing and can definitely work. Still, the posts are
  too short for beginners. Could you please prolong them a little from subsequent time?
  Thanks for the post.

 3. I used to be recommended this web site via my cousin. I’m now not sure whether or
  not this put up is written via him as nobody else recognise such
  detailed approximately my difficulty. You’re wonderful!
  Thanks!

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *