• Tue. Oct 4th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

SATAR MUTANE: AN SAKO DALIBAN JAMI’AR AHMADU BELLO SU 9 BAYAN BA DA KUDIN FANSA

Mako daya bayan sace daliban sashen Faransanci su 9 da wasu mutane da masu satar mutane su ka yi a hanyar Kaduna zuwa Abuja, an samu nasarar sako su bayan biyan kudin fansa.

Daliban dai wadanda ke kan hanyar tafiya cibiyar koyon harshen Faransanci da ke Badagary a Lagos, sun fada komar masu satar, inda a farkon lamarin a ke nemi iyayen su, su biya fansar Naira miliyan 39 kan kowanne dalibi.

‘Yan uwan daliban sun ce sun dage da tattaunawa da masu satar mutanen har ta kai ga cimma ba da diyyar da a ka samu rangwame sakamakon labarin Muryar Amurka da ya fito da batun satar bayan majiyar hukuma ta ce an ceyo kowa, da kuma addu’o’in da a ka yi ta yi.

kudin da a ka biya sun kama daga Naira dubu 400 zuwa dubu 700 kan kowanne dalibi inda a ka sako daliban a kwanar Abuja da ke yankin Kachia a jihar Kaduna.

‘Yar uwar daliban Alheri Akwachim Musa ta ce duk da haka masu satar sun taba lafiyar daliban sanadiyyar jin labarin da Muryar Amurka ta yada.

Jami’in Hulda da jama’a na jami’ar Ahmadu Bello Auwalu Umar ya shaidawa gidan talabijin na Channels cewa an sako daliban kuma sun gamu da dangin su duk da bai ambata ko an biya kudin fansa ba ne ko kuwa a’a.

Daya daga ‘yan uwan daliban ya nuna matukar damuwa da cewa ba su samu wata gudunmawa  da ta taimaka wajen sako daliban ba.

Hanyar Abuja zuwa Kaduna ta zama tarkon sace matafiya da hakan kan sa fasinjoji cika tashar jirgin kasa don samun natsuwa duk da kalubalen samun tikiti da jinkiri.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
2 thoughts on “SATAR MUTANE: AN SAKO DALIBAN JAMI’AR AHMADU BELLO SU 9 BAYAN BA DA KUDIN FANSA”
  1. Hi there! I know this is somewhat off topic but I was wondering
    which blog platform are you using for this website? I’m getting sick and tired of WordPress because I’ve had problems with hackers and I’m looking at
    alternatives for another platform. I would be fantastic if
    you could point me in the direction of a good platform.

Leave a Reply

Your email address will not be published.