Sace daliban makarantar sakanadaren gwamnati ta Maradun a jihar Zamfara su 73 ya yi matukar tada hankali a daidai lokacin da a ke tsammanin samun saukin satar.
Wannan ya zo ne bayan matakan datse samun man fetur da hana barayin sakat da gwamnatin jihar ta dauka.
Rundunar ‘yan sandan jihar ta zuba jami’ai da za su hada kai da sojoji don yunkurin ceto daliban.
Yawaitar sace-sacen ya sa gwamnatin jihar rufe makarantu don ya zama rigakafi ya fi magani na wannan fitina.
Hakanan gwamnatin ta aiyana dokar hana fita na karfe 6 na yamma zuwa 6 na safe a kananan hukumomi 13 inda ta aiyana karfe 8 na yamma zuwa 6 na dare a fadar jihar wato Gusau.
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
Hello, I enjoy reading through your article.
I wanted to write a little comment to support you.
It’s awesome in support of me to have a web site, which is good in favor of my know-how.
thanks admin