• Tue. Oct 4th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

KETARE: SARKIN URDUN LEBANON YA RUSHE MAJALISAR DOKOKI

Sarkin Urdun wato Lebanon Abdullah Bin Hussein ya rushe majalisar dokokin kasar don shirin zaben sabbin ‘yan majalisa a watan nuwamba. A tsarin mulkin Lebanon, za a rushe majalisa a cikin mako don ba da damar gudanar da sabon zabe.

Hukumar zaben Urdun ta tsaida ranar 10 ga watan nuwamba ta zama ranar da za a gudanar da sabon zaben. Sarki Abdullah ya bukaci zaben kasa baki daya bayan kammala wa’adin shekaru 4 na ‘yan majalisar da yanzu a ka rushe.

Urdun kamar sauran manyan kasashen Larabawa na da tsarin Sarauta ko mulkin mulukiyya amma a kan gudanar da zaben ‘yan majalisa a duk bayan shekaru 4.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.