• Tue. Nov 30th, 2021

Noblen tv

Gaskiya Jari…

SARKIN KAJURU YA KUBUTA DAGA HANNUN BARAYIN MUTANE

Sarkin Kajuru a jihar Kaduna Alhassan Adamu ya kubuta daga hannun barayin mutane ba tare da sauran mutanen da su ke tare da shi 13.

An ga jama’a sun yi dafifi a fadar Sarkin don yi masa maraba da dawowa.
Wani faifan bidiyo ya nuna Sarkin mai daraja ta biyu ya fara jawabi sai ya fashe da kuka da ke nuna juyayi da godewa jama’a.

Cikin wadanda su ke hannun barayin da matan Sarkin da yara.
‘Yan ta’addan da majiya ta ce na madugun barayi Baleri ne, sun bukaci kudin fansa naira miliyan 200.
Abun da ya fito fili shi ne a na cigaba da magana da ‘yan barayin don samun kubutar da sauran mutanen da ke hannun su.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *