• Sun. Jan 16th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

SARKI SALMAN YA YI ALLAH WADAI DA YANDA ISRAILA KE RAGARGAZA A GAZA

Sarki Salman na Saudiyya ya yi Allah wadai da matakan da Israila ke dauka na nuna karfi kan Palasdinawa a yankin Gaza da kuma fitinar da ta faro wajen hana Palasdinawa walwala a birnin Kudus.

Sarki Salman na magana ne ta wayar tarho da firaministan Pakistan Imran Khan kan sabuwar fitinar ta Yahudawa da Palasdinawa.

Sarkin ya ce kasar sa na tare da Palasdinawa wajen gwagwarmayar samun hakkin su daga mamaye mu su kasa da Yahudawa su ka yi.

Akalla kimanin Palasdinawa 56 ciki da yara 14 Israila ta kashe a Gaza. Hakanan Israila ta kashe Palasdinawa biyu a yammacin kogin Jodan.

Su ma Palasdinawa a hare-haren su na cilla roka sun kashe Yahudawa 6.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *