Sarki Salman na Saudiyya ya buga hatimin nada sabon ministan aikin haji da na kiwon lafiya da ke da muhimmanci ainun a lamuran aiyukan gwamnatin daular.
An nada Tawfiq Al-Rabiah ya zama sabon ministan aikin hajji da umrah yayin da a ka nada Fahd Aljalajel ya zama sabon ministan kiwon lafiya.
Shi kuma mataimakin ministan sufuri Abdulaziz Ar-Arifi ya rasa mukamin sa, amma an nada shi a matsayin mai ba da shawara a ofishin lamuran ministoci.
Sabon nadi ya hada da Karin girma ga Laftanar Janar Mutlaq Bin Al-Azima ya zama shugaban rundunonin sojan Saudiyya.
Fadar Sarki ta kirkiro sabuwar hukumar raya wasu biranen Saudiyya da su ka hada da Yanbu, Umluj, Al-wajh. Da Duba.
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀