Sarki Salman na Saudiyya ya tattauna da shugaban Amurka Joe Biden kan laifukan yaki da ‘yan tawayen houthi na Yaman ke aikatawa.
Tattaunawar ta gudana ne ta wayar tarho da shugaba Biden ya bugawa Sarki Salman inda su ka yi magana kan hare-haren makamai masu linzami da houthi mai samun goyon bayan Iran ke cillowa cikin Saudiyya.
An ruwaito Sarki Salman na yabawa Amurka don cigaba da marawa Saudiyya baya ga kare kasar ta daga irin wadannan hare-haren.
Shugabannin biyu sun tattauna kan samar da zaman lafiya a yankin gabar ta tsakiya.
Hakanan Sarki Salman ya mara baya ga matakan Amurka na hana kasar Iran mallakar makaman kare dangi na nukiliya.
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
Hello there, You’ve done an excellent job. I will definitely digg it and personally suggest to my friends. I am confident they’ll be benefited from this site.