• Thu. Aug 18th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

SARKI ABDULLAH NA JODAN YA KARBI BAKUNCIN BABBAN JAMI’IN ISRA’ILA

A karo na farko a cikin shekaru 4, Sarki Abdullah na Urdun ko Jodan ya karbi bakuncin babban jami’in Isra’ila da kasar sa ke makwabtaka da ita.
An ga Sarkin da ministan san a harkokin waje Ayman Safadi da daraktan ofishin sa Jafar Hassan tare da ministan tsaron Isra’ila Benny Gentz.
Ganawar ta zo ne sa’a 24 bayan Isra’ila ta dau matakin hana wani dogon zullumi da ya kawo karshen yajin cin abinci da Bapalasdine Hisham Abu Hawash ya yi biyo bayan kama shi da hukumomin Isara’ila su ka yi.
Ganawar ta tabo bukatar Isra’ila da ta tabbatar da zaman lafiya a yankin Palasdinawa da daukar matakin zaman salama mai dorewa ta hanyar kafa kasashe biyu na Paladinawa da Isra’ila.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.