Sarauniyar Ingila Elizabeth ta kamu da cutar korona bairos inda ta ke fama da ‘yar mura don haka a ke kula da lafiyar ta.
Elizabeth mai shekaru 95 ta zama a ajin wadanda za su iya kamuwa da cutar cikin sauki.
Sarauniyar ta kamu da cutar bayan tun farko dan ta mai jiran gado Charles ya kamu da cutar da a ka gano bayan ganawar sa da mahaifiyar ta sa.
A makwan jiya sarauniyar ta yi murnar cika shekaru 70 a kan gado.
An tabbatar da a na yin duk abu mai yiwuwa don shawo kan cutar da ceto ran dattijuwar da ta fi kowa dadewa a gadon sarautar Burtaniya.
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀