Sarauniyar Ingila Elizabeth ta yi murnar cika shekaru 70 kan sarautar Burtaniya a cikin daki ba tare da wani gagarumin buki ba.
Elizabeth mai shekaru 95, ta zama ta farko a tarihin masarautar da ta yi wannan dadewa kan karaga a cikin shekaru 1000 da su ka wuce.
Elizabeth ta hau sarauta a 1952 bayan mutuwar mahaifin ta Sarki George.
Mijin sarautar Yarima Philip yam utu a bara ya na mai shekaru 99 bayan kasancewa a gefen sarauniyar fiye da shekaru 70.
Hatta Yarima mai jiran gado wato dan sarautar Charles shi ne mafi dadewa a jiran sarauta, a yanzu haka ya na da shekaru 73 a duniya.
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀