• Sat. May 21st, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

SANYA HANNU KAN SABUWAR DOKAR ZABE-DA SAURAN RINA A KABA-MASU SHARHI

Biyo bayan sanya hannu da shugaba Buhari ya yi kan sabuwar dokar zabe, masana kimiyyar siyasa da masu sharhi na cewa akwai sauran rina a kaba.
Wannan dari-darin ya shafi sake bukatar da shugaban ya yi ne na a goge sashe 84 na dokar da ya haramtawa masu rike da kujerun siyasa damar zaben ‘yan takara ko tsayawa takarar.
Fassarar wannan sashe na nuna mai son takarar mukami sai ya ajiye kujerar kafin samun damar yin hakan, inda shugaba Buhari ke da matsayar hakan rashin yin adalci ga wadanda ke wannan aji kuma ya sabawa tanadin tsarin mulki.
Masanin kimiyyar siyasa Dr.Farouk BB Farouk ya ce ‘yan majalisar na da hurumin kyale dokar a yanda ta ke ko goge sashen, amma bisa fahimtar juna tsakanin fadar da majalisar.
Shi kuma shaharerren mai hamaiya da tsarin gwamnatin APC Injiniya Buba Galadima wanda ya yi alwashin a fille ma sa kai in shugaba Buhari ya sanya hannu a dokar, ya ce har yanzu shugaban bai sanya hannun da zuciya daya ba kuma dama ya fara batun ne ga dokar da shugaban ya mayar majalisa.
‘Yan siyasar APC da kan su irin jigon ta Musa Abubakar Danmalikin Kebbi sun yi kira ga shugaban ya sanya hannu kan ba tare da cire wasu sassa da su ka hada da zaben ‘yar tinke a tsaida ‘yan takara ba.
Shin majalisa za ta biyawa shugaban bukata ta goge sashen na 84?.
Da alamu majalisar mai shugabancin da ke biyaiya sau da kafa ga shugaban ba za ta gwale shugaban ba ko da za a zarge ta da zama ‘yar amshin shata.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
One thought on “SANYA HANNU KAN SABUWAR DOKAR ZABE-DA SAURAN RINA A KABA-MASU SHARHI”
 1. Hi there, I discovered your site by way of Google whilst looking for a related subject, your web site came up, it seems to be great.
  I have bookmarked it in my google bookmarks.
  Hello there, simply became aware of your weblog via Google, and located that
  it is really informative. I am going to watch out for brussels.

  I’ll appreciate if you proceed this in future. Numerous other
  folks will be benefited from your writing.
  Cheers!

Leave a Reply

Your email address will not be published.