• Wed. May 25th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

SANYA BAKIN SARAKUNA NE KADAI ZAI DAWO DA AREWA KAN TURBA-ALHAJI SHEHU ASHAKA

Dattijo a arewacin Najeriya Alhaji Shehu Ashaka ya ce sanya bakin sarakuna ne zai dawo da arewa kan turba a yayin da yankin ke matukar bukatar salama.
Alhaji Shehu Ashaka da ke magana a Kano, ya ce ya na da kwarin guiwar matukar sarakuna su ka dauki matsayin aikin da Allah ya dora mu su na kula da al’umma, to a cikin wata 6 za a iya samu tsaro mai inganci.
Tun gabanin zuwan turawan mulkin mallaka, Alhaji Ashaka ya ce yankin arewa na hannun sarakuna ne da ke mulki na kulawa da jama’a.
Dattijon ya ja hankalin sarakuna da su sani ba dukiya ba ce kan gaba a abun da su su ka gada a wajen iyayen su, amma sun gaji kula da jama’a ne

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
3 thoughts on “SANYA BAKIN SARAKUNA NE KADAI ZAI DAWO DA AREWA KAN TURBA-ALHAJI SHEHU ASHAKA”

Leave a Reply

Your email address will not be published.