• Sat. May 21st, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

SANI YARIMAN BAKURA YA AIYANA NIYYAR TAKARAR SHUGABANCIN KASA A INUWAR APC

Tsohon gwamnan jihar Zamfara Sani Yariman Bakura ya aiyana cewa zai yi takarar shugabancin Najeriya a inuwar APC.
Tsohon gwamnan ya jagoranci taro na musamman don aiyana niyyar takarar wacce ta biyo bayan wata ganawa da ya yi da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.
Tun a zaben 2019, Sani Yarima na cewa zai yi takara matukar shugaba Buhari ba zai tsaya ba, gas hi yanzu shugaban na shirin kammala wa’adin san a karshe ne na mulki.
Sani Yarima ya ce in an zabe shi zai yi kokarin inganta lamuran tsaro.
A gefe guda shi ma tsohon kakakin majalisar wakilan Najeriya Dimeji Bankole ya shiga jerin masu son takarar a APC.
Tsohon gwamnan Zamfara Mahmud Shinkafi ya jagoarnci tawagar da ta sayawa Bankole fom din takara Naira miliyan 100.
Ba za a yi mamaki ba in masu takara a APC kadai za su iya kai wa mutum 30 kafin rufe sayar da takardun takarar.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
3 thoughts on “SANI YARIMAN BAKURA YA AIYANA NIYYAR TAKARAR SHUGABANCIN KASA A INUWAR APC”
  1. What i do not realize is in truth how you’re now not actually a lot more well-appreciated than you may be right now.
    You’re very intelligent. You recognize therefore significantly when it comes to this subject, made me personally imagine it from so
    many numerous angles. Its like women and men are not fascinated unless it’s one
    thing to accomplish with Lady gaga! Your own stuffs excellent.
    All the time care for it up!

Leave a Reply

Your email address will not be published.