• Mon. May 23rd, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

SANATA RABI’U MUSA KWANKWASO YA SAUYA SHEKA

Sanata Rabi’u Musa kwankwaso ya sauya sheka a hukumance daga babbar jam’iyyar adawa ta PDP zuwa jam’iyyar NNPP.
A wani kwarya-kwaryan taron ganawa da manema labaru a gidan sa da ke anguwar Maitama, a Abuja, Kwankwaso ya ce ya dau matakin ne don yanda wasu a jam’iyyar APC da PDP su ka dau girman kai da ganin in ba da su ba, baa bun da za a iya cimmawa a dandalin siyasa.
Kwankwaso wanda ya fice daga PDP ya ce shugaban jam’iyyar NNPP na mazabar sa a Madobi a Kano ya yi ma sa rejista.
Tsohon gwamnan Kano ya ce ya na sa ran ganin an samu garambawul a siyasar Najeriya a babban zaben 2023 inda za a samu shugabanni da su ka san mutuncin al’umma.
Kwankwaso bai ce zai yi takarar shugaban kasa a inuwar NNPP ba zuwa yanzu, don ya ce shigowar sa kenan don haka bayanai kan haka za su fito daga baya.
Magoya bayan tsohon gwamnan sun nuna mara baya ga sabon matakin da madugun na su ya dauka.
NNPP za ta gudanar da babban taron ta a Abuja a larabar nan

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
2 thoughts on “SANATA RABI’U MUSA KWANKWASO YA SAUYA SHEKA”

Leave a Reply

Your email address will not be published.