• Tue. Oct 4th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

SAMUN ‘YANCI: JIRAGE MASU SAUKAR ANGULU NA SHAWAGI A ABUJA

Jirage masu saukar angulu na shawagi a samaniyar Abuja daidai lokacin da Najeriya ke shirin bukin shekaru 60 da samun ‘yanci daga Burtaniya.
Jiragen dai na dauke da wani kyalle mai dauke da bayanan murnar da ta zo daidai lokacin da Najeriya ta janye tallafin fetur don tsumulmular kudi a yanayin karancin kudin shiga.

Tun daga samun ‘yancin an samu juyin mulki da a ka zubar da jini musamman na 1966 da sojoji  bisa ma’unin kabilanci su ka yi kisan gilla ga wasu daga manyan wadanda su ka karbo ‘yanci kamar firaminista Abubakar Tafawa Balewa, firimiya Sir,Ahmadu Bello da Ladoke Akintola inda shugaban farko Nnamdi Azikwe ya tsira ba a taba lafiyar sa ba.

Cikin shekarun 60 kusan an yi canjaras`na shekarun mulki tsakanin sojoji da farar hula,  sojoji sun shafe kimanin shekaru 30 kan mulki inda farar hula su ka yi mulki na tsawon shekaru 30 duk da biyu daga sojojin da su ka yi mulki sun rikide farar hula su ka sake hawa mulki.

Sabuwar dimokradiyya daga 1999 zuwa bana 2020 ita tafi tsawo a tarihin Najeriya bayan ta farko da ta shekara 6 kacal, yayin da a ka samu shekaru 4 a jamhuriya ta biyu.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
One thought on “SAMUN ‘YANCI: JIRAGE MASU SAUKAR ANGULU NA SHAWAGI A ABUJA”
  1. Genuinely when someone doesn’t be aware of after that its up to other people that they will assist, so here
    it happens.

Leave a Reply

Your email address will not be published.