• Sat. Jul 2nd, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

SAMUN GAWAR MAI ADAWA DA KUNGIYAR HEZBOLLAH LUKMAN SLIM TA JAWO YAMUTSA HAZO A LEBANON

Samun gawar dan gwagwarmaya mai kin jinin kungiyar Hezbollah ta ‘yan shi’a a Lebanon Lukman Slim a yankin kudanci na Zahrani ya jawo yamutsa hazo a kasar ta Larabawa musulmi da kirista.

Kashe dan shi’a mai adawa da kungiyar shi’a, shi ne irin sa na farko a kasar tun 2004.

Kanwar marigayin Basha Al-Ameer ta sanar da bacewar Slim da neman taimakon gano inda ya ke. Labari ya sauya zuwa kisan gilla da a ka yi wa Slim inda a ka samu gawar sa a mota.

Gawar na dauke da harbin albarusai 5 inda 4 su ka samu kan sa 1 kuma bayan sa.

Shugaban kungiyar kare ‘yan jarida ta Lebanon “MENA” a takaice Sheriff Mansour ya ce su na fatan a gano masu hannu a kisan don fuskantar shari’a kuma a na sa ran za a tuhumi kungiyar ‘yan shi’a ta Hezbollah don barazanar da ta rika yi a baya kan daukar ran Slim.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.