• Thu. Dec 1st, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari...

OSINBAJO: ‘YAN SARS DA A KA RUSHE BA ZA SU SHIGA CIKIN SABUWAR RUNDUNA BA

  • Home
  • OSINBAJO: ‘YAN SARS DA A KA RUSHE BA ZA SU SHIGA CIKIN SABUWAR RUNDUNA BA

Mataimakin shugaban Najeriya Yemi Osinbajo ya ce ‘yan rundunar SARS da a ka soke ba za su samu shiga sabuwar rundunar da za a kafa ba wato SWAT.

Osinbajo a sanarwa don rarrashin masu zanga-zanga ya ce ya san irin hushin da su ke ciki kan cin zarafin da ‘yan SARA ke yi da ma karbar toshiyar baki.

Mataimakin shugaban ya ce kwamitin tattalin arziki da ya ke jagoranta ya yi nazarin kafa kwamitocin bincike na shari’a don hukunta wadanda ke da hannu a cin zarafin al’umma.

Manufar sakon shi ne matasan su janye daga zanga-zangar don gwamnati na daukar matakan bin kadun su.
Shugaban majalisar dattawa Ahmed Lawan da kakakin majalisar wakilai Femu Gbajabiamila sun gana da shugaba Buhari kan zanga-zangar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *