• Sun. Jan 16th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

SAMARDA RUWA MAI TSABTA ZAI HANA CUTAR KURKUNU MAI GURGUNTA MUTANE DAWOWA

ByYusuf Yau

Apr 11, 2021

Masana na kara ambatar muhimmancin samarda ruwa mai tsabta a matsayin sahihiyar hanyar hana sake dawowae cutar kurkunu.

Cutar dai kan kama mutane da ke amfani da ruwan kududdufi ko tabkuna inda wani zare mai kamar tana kan fito a kafar wanda ciwon ya kama.

Sanadiyyar kamuwa da ciwon a shekarun baya, mutane da yawa maza da maza sun zama guragu.

Ciwon kurkunu dai shi ne na biyu bayan cutar agana da a ka kawar a duniya. Ba mamaki na uku shi ne cutar shan inna.

Asusun tsohon shugaban Najeriya Yakubu Gowon da hadin guiwar na tsohon shugaban Amurka Jimmy Carter su ka ba da gudunmawae yakar cutar ta kurkunu a yankuna da ke da karancin ruwan sha mai tsabta.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *