• Thu. Dec 9th, 2021

Noblen tv

Gaskiya Jari…

SAMA DA MUTUM MILIYAN 10 KE SHAN TABAR WIWI A NAJERIYA-BUBA MARWA

Shugaban hukumar yaki da shan miyagun kwayoyi na Najeriya Burgediya Janar Buba Marwa ya ce sama da mutum miliyan 10 ke zukar tabar wiwi a Najeriya da hakan ya sa kasar ta fi kowace kasa masu shan wiwi.

Marwa na magana ne a makon yaki da shan miyagun kwayoyi da a ka kaddamar a Abuja.

Buba Marwa ya ce lalle sai kowa ya sa hannu kafin a samu galabar yaki da shan miyagun kwayoyi a Najeriya.

Shugaban na hukuamr NDLEA a takaice ya buakci iyaye su rika caje ‘ya’yan su don fahimtar ko miyagun abokai dun jefa su mu’amala da kwaya.

An yi ittifaki cewa shan kwaya na daga dalilan ta’azzarar lamuran rashin tsaro a Najeriya.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *