• Wed. Dec 1st, 2021

Noblen tv

Gaskiya Jari…

Sama da Mutum 180 ne aka ceto daga hannun ‘yan bindiga a Zamfara

ByAuwal Ahmad Shaago

Oct 8, 2021

Rundunar ‘yan sanda jihar Zamfara ta sanar da ceto sama da mutum 180 wadanda ‘yan fashin daji suka sace a kauyukansu. A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Mohammed Shehu, ya fitar, yace mutanen sun shafe makonni a hannun ‘yan fashin dajin.

An yi nasarar ceto mutanen ne bayan wani aikin nema da ceto da jami’an tsaro suka yi a dajin Tsibiri da ke karamar hukumar Maradun a jihar ta Zamfara. Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan ya ce tuni aka mika mutanen hannun jami’an gwamnati domin kai su asibiti a duba lafiyarsu.

Kan haka BBC ta tuntubi kwamishinan yada labarai na jihar ta Zamfara Ibrahim Dosara don jin a irin halin da aka samu wadannan mutane da aka ceto. Ibrahim Dosara, ya ce an same su cikin yanayi na galabaita sosai, domin da yawa daga cikinsu an same su da kuraje a jikinsu saboda cizon sauro da makamantansu.

Ya ce,” Wasu daga cikin mutanen kuma saboda wahalar da suka sha ko tafiya basa iya yi sai an rike su, sannan kuma mata sun fi maza yawa a cikin mutanen. Kwamishinan yada labaran ya ce, baya ga mata akwai kuma kananan yara na goye duk a cikin mutanen da aka ceto. Ibrahim Dosara, ya yi bayanin cewa an samu nasarar kubutar da wadannan mutanen ne saboda irin matsin lambar da ake yi wa ‘yan fashin dajin, saboda matakan da gwamnatin jihar ta dauka na kakkabe su. Ya ce matsin lambar da suka fuskanta ce ya sa suka gudu suka bar mutanen har aka kai ga gano su a kubutar da su. Kwamishinan ya ce, da zarar an kammala duba lafiyarsu za a kai su domin sada su da iyalansu.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *