• Sat. Nov 27th, 2021

Noblen tv

Gaskiya Jari…

SAM BA ZA MU BI DOKAR HANA FITA TA IPOB BA-‘YAN KASUWAR AREWA A KUDU

‘Yan kasuwar arewa a yankin kudu maso gabashin Najeriya sun ce za su yi biris da dokar da kungiyar ‘yan awaren Biyafara ta IPOB ta aiyana ta hana fita a dukkan ranakun litinin na mako.

Kungiyar da gwamnatin Najeriya ta haramta ta umurci mutane kar su fito a duk ranakun litinin har sai gwamnatin Najeria ta sako shugaban su Nnamdi Kanu.

Shugaban ‘yan awaren dai da ke hannun jami’an tsaron DSS na fuskantar shari’ar cin amanar kasa a gaban kotun Binta Nyako ta babbar kotun Najeriya Abuja.

‘Yan kasuwar musamman na gwari sun ce ba za su zauna a gida kayan su, su rube ba, don haka za su fito kasuwa kamar yanda su ka saba.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *