• Thu. May 19th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

SAM BA MU YARDA DA DAUKI DORA DA MINISTA ADAMU ADAMU YA YI A ZABEN APC NA BAUCHI BA-SARKIN AREWA

ByYusuf Yau

Oct 19, 2021
Jigon APC a Bauchi Alhaji Hassan Sharif ya ce shi da sauran masu ra’ayi irin na sa ba za su taba amincewa da yanda ya yi zargin ministan ilimi Adamu Adamu ya mara baya an nada shugabannin APC na jihar ba.
Kamar yanda a duk Najeriya a ka gudanar da taron zaben shugabannin APC na jihohi, a Bauchi ma an gudanar da hakan amma ta hanyar amincewa a ka karanta sunaye ba tare da kada kuri’a ba.
Sharif wanda shi ma ya nuna sha’awar takarar kujerar ya zargi ministan ilimi Adamu Adamu da cewa gadarar sa da zama mukarrabin shugaba Buhari ya sa ya hada kai da tsohon kakakin majalisar wakilai Yakubu Dogara su ka nada wadanda su ka ga dama a matsayin sabbin shugabanni karkashin Babayo Ali Misau.
Hassan Sharif ya bukaci helkwatar jam’iyyar ta yi watsi da sakamakon ta shirya wani sabon zabe matukar ta na son nasarar jam’iyyar a 2023.
Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.