• Fri. Jul 1st, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

SAM BA MA TARE DA ‘YAN IPOB- TUBABBUN NEJA DELTA

Tsagerun Neja Delta da su ka tuba da samun ahuwa zamanin mulkin marigayi shugaba Umaru Musa Yar’adua sun nesanta kan su da hannu a lamuran ‘yan awaren Biafra na IPOB da ke zubar da jini don kafa kasar su.

Tsageran na cewa ba abun da ya hada su dan’yan IPOB da ke.

‘Yan awaren na nuna kamar su na aiki da tsoffin tsageran na Neja Delta da sanya yankin Neja Delta a taswirar kasar da su ke mafarkin kafawa.

A na samu  takaddama don kabilun yankin Neja Delta ba za su amince ‘yan kabilar Ibo na kudu maso gabar su danne su a lamarin Biafra ba.

Hatta sunan Biafra an dauko shi ne daga harshen Ibo da ya saba da kabilu daban-daban na Neja Delta irin Ijaw, Itsgekiri da sauran su

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
57 thoughts on “SAM BA MA TARE DA ‘YAN IPOB- TUBABBUN NEJA DELTA”

Leave a Reply

Your email address will not be published.