Kwana daya bayan kawar da gwamnatin rikwan kwarya ta mika mulki hannun farar hula a Sudan, shugaban mulkin soja Janar Abdel Fattah Burhan ya ce shi sam ba juyin mulki ya shirya ba.
Janar Burhan ya ce soja sun dau matakin inganta hanyar mika mulki ne a hannun farar hula kuma ba a sauya komai ba bisa yarjejeniyar 2019 da ta tsara maida mulkin a 2023.
Burhan ya kara da cewa firaminista Abdallah Hamdok da a ka kawar na gidan sa ( wato gidan Burhan din) don tsare lafiyar sa kuma zai koma gida bayan kafa sassan da za su cigaba da jagorantar kasar.
Hakanan Burhan ya kara da cewa za a janye dokar ta baci in lamura su ka daidaita.
Jagoran sojan ya ce matakin sojan don amfanin al’ummar Siudan ne.
Sudanawa da dama na gudanar da zanga-zanga inda zuwa yanzu a ke raderadin mutum 7 sun rasa ran su a wajen tunzurin.