• Mon. Jul 4th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

SAM BA BA A MIKAWA BABBAN SUFETO RAHOTO KAN ABBA KYARI BA-RUNDUNAR ‘YAN SANDA

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta ce kwamitin bincike kan zargin da hukumar binciken aiyuka ta Amurka ta yi wa Abba Kyari bai mika rahoton sa ba.

Babban sufeton ‘yan sanda Usman Baba Alkali ya kafa kwamitin don gano gaskiyar zargin aikata ba daidai ba daga Abba Kyari bisa huldar sa da dan damfara Ramon Abbas Hushpuppi.

In za a tuna tuni rundunar ta dakatar da Kyari da nada Tunde Disu ya maye gurbin sa a rundunar babban sufeton ‘yan sanda ta aiki da cikawa.

Kakakin rundunar Frank Mba ya ce da zarar an kammala binciken za a sanarwa jama’a don labarin da wasu kafafe su ka yada na nuna an fito da rahoto har Kyari ya yi tayin murabus ba gaskiya ba ne.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.