• Sun. Dec 5th, 2021

Noblen tv

Gaskiya Jari…

SAKONNIN WAYAR TARHO TA JAWO ZARGIN ABBA KYARI DA TUHUMAR DAN DAMFARA HUSHPUPPI

Sakonnin wayar tarho da hukumar bincike ta taraiya a Amurka FBI ta duba su ka sa zargin shaharerren dan sanda Abba Kyari da hulda da dan damfara Ramon Abbas da a ka fi sani a yanar gizo da Hushpuppi.

Duk da Kyari ya fitar da sanarwar kare kan sa da nuna sam bai aikata wani laifi ba, hujjojin da FBI ta fitar ka iya saka tuhuma ko zargin aikata kuskure ko ba bisa ganganci ba daga Abba Kyari.

Hushpuppi ya amince da zargin damfarar dan kasuwar Dubai fiye da dala miliyan daya da nuna shi ma’aikacin banki ne a Amurka da amfani da suna Malik.

Za a jira sakamakon binciken rundunar ‘yan sandan Najeriya kan zargin da ke haddasa muhawara tsakanin magoya baya da masu hamaiya da Kyari.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *