• Fri. Oct 7th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

SAKON KUKAH NA CIGABA DA TADA KURA KAN NEMAN JUYIN MULKI DA FAKEWA DA BATUN ADDINI

Sakon ranar kirismeti da shugaban darikar katolika na kirista a Sokoto Bushop Mathew Hassan Kukah, kan gwamnatin shugaba Buhari na kara tada kura don yanda bayanin ya kunshi addini da bangaranci.

Kukah dan asalin jihar Binuwai mazaunin Sokoto a yanzu don zama Manzon cocin katolika, ya ce da a ce dan kadan daga lamuran da su ka rincabe yanzu a Najeriya sun auku ne karkashin shugaba da ba musulmin arewa ba, da an yi juyin mulki.

Wannan sako na Kukah ya jawo martani na cewa ya na zugawa ne don wa imma a yi juyin mulki ko al’ummar kudu su tsani na arewa.

Gwamnatin Najeriya ta yi watsi da sakon na Kukah da nuna bai dace shugaban addini su rika kunsa kalaman da ka iya kawo fitina ba.

Shi ma Kukah ya sake fitowa don karin bayani kan sakon da cewa ba wai ya na kira a yi juyin mulki ba ne, amma ya damu ne da tabarbarewar tsaro.

Kukah ya kara da cewa ba shi da wani sabani da shugaba Buhari.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
4 thoughts on “SAKON KUKAH NA CIGABA DA TADA KURA KAN NEMAN JUYIN MULKI DA FAKEWA DA BATUN ADDINI”
 1. After exploring a number of the blog posts on your web
  site, I really like your technique of blogging.
  I book-marked it to my bookmark webpage list and will be checking back soon. Please visit my website as well and let
  me know how you feel.

 2. Your mode of describing everything in this post is genuinely nice,
  all be able to effortlessly understand it, Thanks a lot.

 3. Hi, I do think this is an excellent website. I stumbledupon it 😉 I
  will return yet again since I book-marked it. Money
  and freedom is the best way to change, may you be
  rich and continue to help others.

Leave a Reply

Your email address will not be published.