• Thu. Dec 9th, 2021

Noblen tv

Gaskiya Jari…

SAKE EL-ZAKZAKY – KADUNA ZA TA DAUKAKA KARA

Gwamnatin jihar Kaduna za ta daukaka kara kan hukuncin babbar kotun jihar da ya sake jagoran ‘yan shia Ibrahim El-zakzaky da matar sa Zeenatu.

Alkalin kotun Gideon Kurada ya amince da bukatar lauyoyin El-zakzaky na sake shi ba tare da samun sa da laifi ba, da hujjar a 2017 a ka tsara dokar da ta samu El-zakzaky da laifin da ya aikata a 2015.

Gwamnatin Kaduna ta gurfanar da El-zazzaky a kotu ds tuhumar tada hankalin al’umma, haramtaccen taro da ma kashe wani soja a lokacin arangamar ‘yan shia da dakarun tsaron tsohon babban hafsan sojan Najeriya Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai.

Yanzu dai gwamnatin ta Kaduna ta karbi takardun hukuncin alkali Kurada da ta ce ya yi kuskuren fahimta kuma za ta daukaka kara.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *