• Thu. May 19th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

SAKAMAKON ZABEN KANANAN HUKUMOMI A ABUJA NA NUNA APC DA PDP DUK SUN SAMU NASARA

Sakamakon zaben kananan hukumomin babban birnin Najeriya Abuja na nuna manyan jam’iyyu biyu na APC da PDP sun samu nasarar samun lashe kananan hukumomi.
Zaben wanda hukumar zabe ta kasa INEC kan gudanar, bai samu fitowar masu kada kuri’a ba, inda akalla a wani akwai ma a ka ba da labarin ba wanda ya kada ko da kuri’a daya tak.
Sakamakon zaben na nuna babbar jam’iyyar adawa ta PDP ta karbi wasu kujeru daga jam’iyyar APC mai mulki tamkar an yi canjaras.
Abuja na da kananan hukumomi 6 da su ka hada da karamar hukumar tsakiyar birni mai suna AMAC a takaice.
Masu sharhi na cewa akwai bukatar kara karfafawa jama’a guiwa su rika fitowa zabe da karbar rejistar su don zaben wanda su ke so a babban zaben kasa na 2023SAKAMAKON ZABEN KANANAN HUKUMOMI A ABUJA NA NUNA APC DA PDP DUK SUN SAMU NASARA
Sakamakon zaben kananan hukumomin babban birnin Najeriya Abuja na nuna manyan jam’iyyu biyu na APC da PDP sun samu nasarar samun lashe kananan hukumomi.
Zaben wanda hukumar zabe ta kasa INEC kan gudanar, bai samu fitowar masu kada kuri’a ba, inda akalla a wani akwai ma a ka ba da labarin ba wanda ya kada ko da kuri’a daya tak.
Sakamakon zaben na nuna babbar jam’iyyar adawa ta PDP ta karbi wasu kujeru daga jam’iyyar APC mai mulki tamkar an yi canjaras.
Abuja na da kananan hukumomi 6 da su ka hada da karamar hukumar tsakiyar birni mai suna AMAC a takaice.
Masu sharhi na cewa akwai bukatar kara karfafawa jama’a guiwa su rika fitowa zabe da karbar rejistar su don zaben wanda su ke so a babban zaben kasa na 2023

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.