• Thu. May 19th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

SAKAMAKON WASANNIN DAREN LITININ 4TH/4/2022 NA LALIGA DA PREMIER

Crystal palace sunyi wasan kura da arsenal
A daren litinin crystal palace sun karbi bakuncin arsenal. Mintuna goma sha shida da take wasan, dan wasan crystal palace wato phillipe mateta ya zura kwallo a ragar Arsenal a minti na 26 Jordan ayew ya zura kwallo ta biyu sannan a minti na 74 Wilfred Zaha ya zura kwallo ta uku a ragar Arsenal a bugun daga kai sai mai tsaron gida.
Samun nasarar crystal palace yasa sun matsa daga mataki na 13 zuwa mataki na 9.
A can kasar sifaniya, real socieded sun karbi bakuncin espanyol.
Wasa tsakanin real socieded da espanyol an kai har tsawon mintuna 90 ana ba hamata iska ba tare da wani ya samu nasarar zura kwallo ba, sannan real socieded suka samu bugun daga kai sai mai tsaron gida, inda dan kwallon real socieded Alexander Isak ya zura kwallo a ragar espanyol haka aka tashi wasan.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
One thought on “SAKAMAKON WASANNIN DAREN LITININ 4TH/4/2022 NA LALIGA DA PREMIER”
  1. Hi, I think your website might be having browser compatibility issues. When I look at your blog site in Safari, it looks fine but when opening in Internet Explorer, it has some overlapping. I just wanted to give you a quick heads up! Other then that, very good blog!

Leave a Reply

Your email address will not be published.