• Mon. May 23rd, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

SAI YANDA HALI YA YI, YAYIN DA ASUU TA ZARCE DA YAJIN AIKI

ByNoblen

Mar 15, 2022

Yanzu dai daliban jami’a a Najeriya sun shiga mawuyacin yanayi, yayin da malaman jami’ar su ka zarce da yajin aiki da mako 8.
Kungiyar malaman ASUU ta baiyana zarcewa da yajin ne bayan karewar yajin aikin gargadi na tsawon wata daya.
AA taron kungiyar a jami’ar Abuja, shugaban kungiyar Farfesa Emmanuel Osodeke ya ce gwamnati ba ta mutunta lokacin yajin aikin gargadin wajen daukar matakan sulhu ba.
Osodeke ya ce ASUU ta kars mako 8 don ba wa gwamnati karin damar daukar matakan da za su mutunta yarejeniyar da a ka yi da ita da ta faro daga watan disambar 2020.
Alamu na nuna ASUU na shirin tafiya wani dogon yajin aiki ne matukar mako 8 su ka cika ba da samun sulhu da gwamnati ba.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
One thought on “SAI YANDA HALI YA YI, YAYIN DA ASUU TA ZARCE DA YAJIN AIKI”

Leave a Reply

Your email address will not be published.