• Wed. Dec 1st, 2021

Noblen tv

Gaskiya Jari…

SAI AN SHIGAR DA WAYAR DA KAI GIDAJE KAFIN SAMUN NASARA-MASU SHARHI

Yayin da kalubalen tsaro ke shafar kowane bangare fiye da na ‘yan ta’adda, masu ruwa da tsaki da ba da shawarar isar da sakonnin zaman lafiya gidaje tun daga matakin kauyuka don hakan ne zai samar da maslaha.

Wannan dai don ba ya ga kashe-kashen ‘yan ta’adda, a ke samun bunkasar kiyaiyar kabilanci da bambancin addini.

Da ya ke sharhi kan fitar kabilanci da bambancin addini da musamman ke addabar wasu sassa na arewa ta tsakiyar Najeriya, tsohon gwamnan Kano Mallam Ibrahim Shekarau ya ce wa’azin zaman lafiya a masallatai da majami’u ba zai wadatar wajen gujewa fitinar cikin al’umma ba.

Mallam Shekarau ya ce kafa rundunar Hizba ya yi tasiri wajen yakar miyagun aiyuka tun kafin a makara a Kano, amma a wasu jihohin musamman da abun da ya faru na hallaka matafiya kwanan nan a Filato, sai an sauya sabon salo.

Tun a fitinar baya ta tare matafiya, shugaban matasan kungiyar kiristoci CAN reshen arewa Evengelist Musa Misal ya nesanta addini daga mummunar dabi’ar.

Najeriya dai kasa ce mai bambancin addini da yawan kabilu da ke kokarin zaman tare da sanya hannun kowane bangare a majalisa da gwamnatin tsakiya a Abuja amma tamkar a na tufka wasu na warwara.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *