Daya daga dattawan arewa kuma fitaccen dan kasuwa Alhaji Shehu Ashaka ya ce sai an nuna ba sani ba sabo kafin kawo karshen masu kisan gilla a jihar Filato.
Alhaji Ashaka wanda ya ke nuna juyayi ga kashe matafiya a yankin Bassa, ya ce masu kisan na da kwarin guiwar yin abun da su ka ga dama ne don ba sa fuskantar hukunci daidai laifin da su ka aikata.
Alhaji Ashaka wanda fitinar Jos ta yi sabadiyyar konawa gida kurmus a shekarun baya, ya buksci lalle gwamnati ta dau hukuncin da ya dace kan masu laifin da a ka cafke don hakan ya zama gargadi ga sauran masu son zubar da jini a nan gaba.
Dattijon wanda ya raba motocin daukar gawa a dukkan kananan hukumomin jihar, ya ce ba wata kabilar da za ta iya korar wata daga Filato don wata gadarar son zuciya.