• Mon. Jan 17th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

SABUWAR SHEKARA 2022-ALHERIN GABA YA FI NA BAYA YAWA-SHUGABA BUHARI

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nuna duk da kalubalen da kasar ke fuskanta ta tsaro da cikas din korona, amma gwamnatin sa ta samu nasarori da dama.
Shugaba Buhari ya ce abun da ya faru a baya ya wuce, amma alherin da ke gaba mai darajar gaske ne.
A rubutaccen sakon shugaban na sabuwar shekara ta 2022 mai sakin layi 15, ya ce a matsayin sa na mutum kazalika kuma shugaban kasa ya na damuwa ainun da yanda a ke samun tabarbarewar tsaro, ya na mai ta’aziyya ga ‘yan uwan jami’an tsaro da fararen hula da su ka rasa ran su sanadiyyar fitinar.
Shugaba Buhari wanda ya ce ya samar da kayan aiki da sake salon rundunonin tsaro don kare rayuka da dukiyar al’umma, ya nuna gwamnatin ba za ta yi kasa a guiwa ba don lamuran tsaro na kan gaba a lamuran da ya fi maida hankali a kai.
Muhammadu Buhari ya jinjinawa majalisar dokoki don amincewa da dokar sashen man fetur PIB  a takaice da ta yi garambawul ga sashen; ya na mai cewa a bana gwamnatin sa za ta kara maida hankali kan kimiyyar yanar gizo wajen fadada hanyoyin tattalin arziki.
Ga shugaban matasa na tsohuwar jam’iyyar CPC da shugaba Buhari ya kafa Abubakar Maikudi ya ce duk abun da shugaban ya aiwatar in dai ba ya bin sawu ba za a samu tasiri ba.
Shi kuma jigo a kamfen din shugaban Aminu Madaucin Bakori ya aza alhakin wasu matakan da ke jawowa shugaban suka da rashin tasiri kan mukarrabai.
Shugaban dai zai share shekarar da bin kasafin kudi na Naira tiriliyan 17.1, ya yi kwafa kan yanda ‘yan majalisa su ka cusa aiyuka 6,576.
Hakan na nuna kusan kowane dan majalisa zai tashi da kimanin aiyuka 14 kasancewar yawan dukkan ‘yan majalisar 469 ne.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *