• Sun. Jan 16th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

SABON SHUGABAN NIJAR BAZOUM YA GANA DA SHUGABA BUHARI

Sabon shugaban Nijar Mohamed Bazoum ya ziyarci fadar Aso Rock inda ya gana da shugaba Buhari.

Wannan ita ce ziyara ta farko bayan shan rantsuwar sa a farkon watan nan a birnin Yamai.

Tsohon shugaba Muhammadou Issofou ya shigo Abuja a karshen watan febreru don bankwana da madafun iko da kuma a ka yi amfani da wannan dama wajen radawa wani titi a Abuja sunan sa.

Da alama dai ziyara ce kawai ta zumuncin kasashen biyu makwabta na Afurka ta yamma.

Kazalika hakan ka iya nuna Najeriya na mara baya ga Bazoum ba PNDS duk da watsi da aiyana shi a matsayin wanda ya lashe zabe da ‘yan adawa na RDR karkashin Mammane Ousmane su ka yi.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *