• Wed. May 25th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

SABON SARKIN ZAZZAU AHMAD NUHU BAMALLI YA SHIGA GIDAN SARAUTAR ZAZZAU

Sabon sarkin Zazzau Alhaji Ahmad Nuhu Bamalli ya shiga gidan sarautar Zazzau a matsayin sarki na 19 daga dangin mallawa.Bayan kimanin kwana 18 da rasuwar sarkin Zazzau Shehu Idris, gwamnan jihar Kaduna Nasiru Elrufai ya amince da nada Ambasada Ahmad Nuhu Bamalli a matsayin sabon sarkin Zazzau.

Duk mutum 3 da masu zaben sarki su ka jera sunayen su don samun sarautar, ba su samu shiga ba don canko Bamalli da gwamna El-rufai ya yi wanda dama mutumin sa ne.Da yawa a yanar gizo an fi yayata sunan Yariman  Zazzau Munir Jafar da zama mafi cancanta a neman saruatar.

Cikin wadanda masu zaben sarki su ka sanya sunan sa har da dan marigayi sarki shehu Idris.Yanzu dai da alamu duk hankali ya kwanta tun da an samu sabon sarkin babbar masarautar a jihar Kaduna da ma ta ke cikin masu tagomashi a tarihin arewacin Najeriya.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.