• Fri. Oct 7th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

SA’AD HARIRI YA JINGINE BATUN ZAMAN SA FIRAMINISTAN LEBANON BAYAN WATANNI NA RASHIN TABBAS

ByNoblen

Jul 16, 2021 , ,

Firaministan Lebanon mai jiran ya hau gado Sa’ad Hariri ya sauka daga mukamin bayan waranni a na shan dambarwa da rashin tabbas a kasr.
Hariri ya ba da dalilan rashin jituwa kan wasu lamura da shugaban kasar Michel Aoun ya sanya shi daukar matakin.
Wannan rashin tabbas zai iya jefa Lebanon cikin karin matsalolin kuncin tattalin arziki da bankin duniya ya ce ba a sake ganin irin sa a duniya ba tun shekaru 150 da su ka wuce.
Bayan kamar ganawa ta miniti 20 da Aoun, Hariri ya ce ta baiyaba karara ba zai iya daidaitawa da shugaban ba.
Dama Hariri ya ce zai ajiye aikin a alhamis din nan matukar bai samu jituwa da Aoun ba kan majalisar minidtoci ta mutum 24 da ya mika ma sa da ke da sabbin mutane.
Shugaba Aoun ya ce Hariri ya ki amincewa a tattauna da shi ka gyare-gyare a sabuwar gwamnatin da ya ke shirin kafawa.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
2,989 thoughts on “SA’AD HARIRI YA JINGINE BATUN ZAMAN SA FIRAMINISTAN LEBANON BAYAN WATANNI NA RASHIN TABBAS”