• Mon. Jul 4th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

RUWAN SAMA YA FARA ZAMA A SASSAN NAJERIYA SAI HARAMAR NOMA

ByYusuf Yau

Jun 16, 2021 , ,

Sassan Najeriya daban-daban musamman na arewa na baiyana samun ruwan sama mai yawa a ‘yan kwanakin nan.

Ruwan ya samu a wasu sassa da su ka kwan biyu sai hadari da tsananin zafi amma ba ruwan.

Za a iya cewa abubuwa biyu ne kananan manoma ke magana a matsayin kalubalen da ke barazana ga noma a bana da su ka hada da tsadar taki da kuma kalubalen tsaro.

Yayin da taki ke zama in manomi ya na da kudi zai iya samu ko kuma ya yi rance, tsaro ya zama babbar barazana don a wasu sassan manoma na fargabar shiga kungurmib daji don noma saboda yiwuwar fadawa tarkon masu satar mutane.

Noma a can cikin dajin da a ke fargabar ya fi yabanya don can a ke samun kasar da ba ta gaji ba don haka da taki dan kadan za a samu amfanin gona mai yawa.

Wannan ya nuna bukatar gwamnatoci a dukkan matakai su dau matakin samar da wadataccen taki mai rangwame da kuma tura jami’ai su na sintiri ko daukar matakin gaggawa da zarar an ji labarin bullowar wasu miyagun iri.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.