• Fri. Oct 7th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

RUWAN SAMA BA YANKEWA YA NA SAUKA A ABUJA DUK KARSHEN MAKO

Ruwan sama ba yankewa na sauka a Abuja hatta lokacin da mu ke rubuta wannan labari inda ko ina ya jike jagab da ruwan da zai yiwa shuka amfani ainun.

Tun shigowa watan nan na agusta, ba a samu irin wannan ruwan ba da ya shafi kowane sashe na birnin inda mutane su ka dauko lema don samun shiga shaguna da sauran sassa na hada-hadar yau da kullum.

Da hasken safiya a ka rika ganin duru-duru irin na asubahi da ya sa mutane kunna wutar mota don gujewa aukuwar hatsari.

Hakika direbobi marar sa na’urar sanyaya mota da za ta iya goge numfashi daga jikin gilashin sun sha fama don kokarin tuki a yanayin mai wuyar tafiya daidai ba tare da fadawa fargaba ba.

Masu sayar da robobin goge gilashi na baje hajar su don ganin kasuwa ta bude a sakamakon wannan ruwa mai yawa.

Tabbas da dai Abuja ba ta da layukan wucewar ruwa nakarkashin kasa, da za a iya samun gagarumar ambaliyar ruwa.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.