• Sat. Jul 2nd, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

RUNDUNAR ‘YAN SANDAN NAJERIYA TA CAFKE MASU SATAR MUTANE DA FYADE A FATAKWAL

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta ba da labarin cafke wasu miyagun iri biyar a Fatakwal jihar Ribas wadanda su ka yi kaurin suna wajen satar mata da neman kudin fansa.


Miyagun guda biyar sun gwanance wajen fyade ga matan da su ka sace da kuma karbar kudin fansa daga iyalan su.


Mutanen sun hada da Osinachi Ngwakwe mai shekaru 22, Sammy Junior mai shekaru 27, Epo-Bari Nwolu mai shekaru 26, Yabari Gbarale mai shekaru 29 sai Barine Yilda mai shekaru 30.


Bincike ya gano miyagun kan faki mata ne masu tuka motoci masu tsada su bi su inda ba mutane sosai su yi awun gaba da su zuwa maboyar su, su yi ta yi mu su fyade daga bisani su karbi kudin fansa daga iyalin su.


Hakanan su kan sayar sa motocin masu tsada na matan da su ka ciwa zarafi.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.