• Fri. May 20th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

RUNDUNAR ‘YAN SANDA TA NAJERIYA TA NADA SABON KAKAKI CSP OLUMUYIWA ADEJOBI

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta nada sabon kakakin ta CSP Olumuyiwa Adejobi, wanda tsohon kakakin rundunar ne a jihar Ogun.
CSP Adejobi zai amshi ragama daga Frank Mba wanda babban sufeton ‘yan sanda ya sanya sunan sa a jerin sunayen jami’an da za a tura cibiyar karin kwarewar aiki ta jami’an gwamnati da ke Kuru a jihar Filato.
Frank Mba ya rike mukamin kakakin rundunar a karo biyu wato wannan lokaci da zai mika ragama da kuma zamanin tsohon babban sufeto MD Abubakar.
In a na tuna sunayen jami’an labarum rundunar a ‘yan shekarun dimokradiyyar nan, sai dai a kwatanta sunan Mba Emmanurel Ojukwu inda ba mamaki Moshood Jimoh zai mara mu su baya.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.